fidelitybank

Muna neman afuwa a kan rufe kafafen yada labarai – Gwamnatin Zamfara

Date:

Gwamnatin Jihar Zamfara ta nemi afuwa kan rufe kafofin yaɗa larabai shida da ta yi.

Jaridar The Cable a Najeriya ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta bayar da umurnin rufe wasu kafofin yada labarai a Gusau, babban birnin jihar saboda yada shiri ka yakin neman zabe da Jam’iyyar PDP ta gudanar.

Kafofi yaɗa labaran da abin ya shafa sun ƙunshi Radio Najeriya, da Pride FM Gusau, da NTA Gusau, da Gamji Talabijin, da Vision FM, da Al Umma TV.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamna Bello Matawalle ya sanar da dokar kulle a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da kuma Gummi na jihar bayan ɗawowar hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamna Matawalle ya kuma bayar da umurnin dakatar da tarukan siyasa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Shima da yake magana kan batun, Abdullahi Shinkafi, shugaban kwamitin hukunta ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifi, ya nemi afuwar kafofin yada labaran yayin tattaunawa da manema labarai a jiya Litinin.

Shinkafi ya ce tuni gwamnati ta janye umurnin da kwamishinan ‘yan sanda ya bayar na kamawa tare da hukunta mutane da aka gani a kafofin yaɗa labaran.

Ya kuma bukaci gidajen yaɗa labaran da kuma ‘yan jarida da su mutunta dokokin jihar da kuma taimaka wa gwamnati a kokarinta na dakile ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe ƴan ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...
X whatsapp