fidelitybank

Mun sauya fasalin kudi saboda barayin da suka boye su – Buhari

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa, gwamnati za ta tabbatar da cewa, ‘yan ƙasa ba su sha wahala ba ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofiin takardun kuɗinsu da sabbi a yayin da wa’adin da babban bankin ƙasar ya saka ke ƙara ƙaratowa.

Yayin da yake martani game da rahotonni dogayen layukan mutanen da ke shafe sa’o’i domin samun musanya tsoffin kuɗinsu a bankuna, lamarin da ya janyo suka daga ɓangarorin adawa a ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa an fito da batun sauya fasalin kuɗin ƙasar ne domin yin maganin mutanen da suka ɓoye kuɗin haram, ba don cutar da talaka ba.

Ya kuma ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da ɗaukar nauyin ta’addanci da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Shugaba Buhari ya kuma ce tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar

Game da wahalhalun da talakawa ke sha na musanya kuɗaɗensu kuwa, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin taimaka musu wajen musanya kuɗaɗensu.

Ya kuma jaddada cewa babban bankin ƙasar da sauran bankunan ƙasar sun ƙara haɓaka hanyoyin musanya wa mutane kuɗaɗensu domin tabbatar da cewa an musanya wa kowa kuɗinsa kafin cikar wa’adin.

Babban bankin ƙasar dai ya saka ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar ƙarshe ta daina amfani da tsoffin takardun kuɗi na 200 da 500 da kuma 1000 a faɗin ƙasar.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp