fidelitybank

Mun sa an rage Data akan 1G Naira 350 daga Naira 1,200 – Pantami

Date:

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Pantami, ya ce, an rage matsakaitan farashin bayanai na Gigabyte daya na Data zuwa N350 a watan Oktoban 2022 daga N1200 a watan Nuwamba 2019.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a wajen rufe taron Maiden Digital Economic Regional Conference, DERC, wanda aka gudanar a Abuja.

Pantami, yayin da yake magana kan nasarorin da gwamnatin tarayya ta samu a fannin watsa labarai, ya ce da kaddamar da kamfanin Elon Musk’s Starlink, a yanzu Najeriya tana da kashi 100 cikin 100 na shiga cikin kasar baki daya.

Karanta Wannan: Mun dakile kutse 66 daga yankin Turai – Pantami

Ya bayyana cewa, sauran kasashen yammacin Afirka suna da sha’awar daukar manufofin tattalin arzikin dijital na kasar a duk fadin yankin.

A cewarsa, “Idan ka lura da tsarin, matsakaicin farashin data gigabyte daya ya kai Naira 1,200 a watan Nuwambar 2019, sai muka ce nan da 2025 muna sa ran rage shi zuwa N390 ta hanyar rage farashin kayayyakin da ake samarwa. A yau, bisa ga rahoton Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, a watan Oktoba 2022, matsakaicin farashin 1GB na bayanai yanzu ya zama N350. Wani lokaci abin da muke yi a cikin tsara manufofin shi ne rashin cika alkawari da wuce gona da iri.”

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp