Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin tarayya ta kashe naira biliyan 9 domin gyara layin lantarkin Shiroro-Mando-Kaduna.
Layin ne ya lalace a watan Nuwamban bara, wanda ya yi sanadiyar ɗauke wuta a jihohi 17 na arewacin Najeriya, sannan kuma layin da ya maye gurbinsa shi ma ɓatagari suka lalata shi kafin aka gyara.
Ministan ya bayyana a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji ya fitar, cewa har yanzu ba a gama gyara layin ba.
“Kamfani samar da wutar lantarki ya kashe sama da naira biliyan 9 domin gyara turakun rarraba lantarkin da ƴanbindiga suka lalata a layin lantarkin Shiroro-Mando-Kaduna, wanda ya jefa mafi yawan yankin arewacin Najeriya duhu a bara. Har yanzu ba mu kammala gyarar ba saboda rashin tsaro,” in ji shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A game da kasafta naira biliyan 8 domin wayar da kan ƴan Najeriya kan biyan kuɗin wuta a kasafin kuɗin 2025, ministan ya za a yi amfani da kuɗin ne domin wayar da kai, da ilimantarwa da kuma samar da fasahar zamani domin kare kadarorin makamashi.