Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce bayannan leken asirinta ya nuna cewa harin bam da ƙasar ta kai wa Iran a watan da ya gabata ya janyowa shirin nukiliyar ƙasar koma baya na shekara biyu.
Kakakin ma’aikatar Pentagon Sean Parnell ne ya gabatar da waɗannan bayanan.
Shugaba Trump ya dage kan cewa hare-haren da Amurka ta kai sun lalata cibiyoyin nukiliyar Iran baki ɗaya.
A wani ɓangare kuma, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta soki Iran kan matakin da ta ɗauka na dakatar da hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya a hukumance, inda ta bayyana hakan a matsayin matakin da bai dace ba.