Wata motar Tirela ta kashe wasu yara ‘yan makaranta a tashar mota ta makarantar Grammar da ke unguwar Ojodu Berger a birnin Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa, motar ta kwacewa direban, wanda ya haifar da mumunan hadarin.
Rahotanni da ba a tabbatar da su ba, sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya kai tsakanin 15 zuwa 20, duk da cewa Politics Nigeria ta rawaito cewa, ba ta iya tantance ainihin adadin mutanen ba.
Daliban da abin ya shafa na komawa gida bayan rufe makaranta.
Wani ganau ya ce wasu mutane bata gari sun kashe direban motar da ya haddasa hadarin. An kuma kona motar.