Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar da su rinka sanya kasar nan cikin addu’o’in samun zaman lafiya.
Alhaji Aminu Ado Bayero, bukacin hakan ne lokacin da kasar nan ke ciki a kan matsalar tsaro da ke fuskanta.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin gudanar da maulidi Annabi Muhammadu (S.A.W) daya gudana a fadar sarkin a Kano.
A nasa jawabin shugaban kungiyar sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero zabi sonka Entertainment, Alhaji Shariff Atiku Kabir, ya kuma addu’ar samun zaman lafiya mai daurewa.
Taron Maudidin ya samu halartar mutane da dama cikin masaruta da wajen ta.