Sakataren tsaron Amurka Llyod Austin ya nuna goyon baya ga takwaransa na Isra’ila Yoav Gallant kan dalilan kaddamar da hari ta kasa a Lebanon.
Ma’aikatar tsaro ta ce mutanen biyu sun amince da bukatar ruguza duk wani wuri da ake kaddamar da hare-hare a kan iyakar Isra’ila da Lebanon.
“Manufar hakan ita ce tabbatar da cewa Hezbollah ba ta samu damar sake maimaita irin harin da Isra’ila ta gani ba a yankunanta na arewaci.
Wakilin BBC ya ce abin da wannan ke nufi shi ne Amurka tana bai wa Isra’ila cikakken goyon bayan kan hare-haren da take kaiwa a Lebanon.
Sanarwar ta kuma ce Mista Austin ya jadadda gargaɗi ga Iran cewa za ta dandana kudarta muddin ta kaddamar da hari kai-tsaye a kan Isra’ila.


