fidelitybank

Mazauna Ketare: ‘Yan Najeriya miliyan 1.5 a Italiya ba su da fasfo – NIDOE

Date:

Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, a nahiyar Turai (NIDOE), reshen kasar Italiya, ta ce kimanin mutane miliyan 1.5 daga cikin miliyan 3 da su ka yi wa rijista a Italiya na fama da karancin fasfo din Najeriya.

Shugaban kungiyar, George Omo-Iduhon, ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai yayin da ya ke tunani kan ayyukan NIDOE a Turai da Italiya.

An amince da NIDOE a matsayin dandalin hukuma wanda ’yan Najeriya mazauna kasashen waje za su iya gabatar da kokarinsu na ci gaba a Najeriya.

Ƙungiyar ta na haɗin gwiwa tare da al’ummar Najeriya da ƙungiyoyin ƙwararru da kuma kasuwancin jama’a da masu zaman kansu a cikin wuraren da a ka mayar da hankali kamar su ƙwararrun a saka hannun jari na waje (FDI) da shawarwarin masu ruwa da tsaki da ayyukan likitanci da tallafin ilimi da kwarewa wajen sauya wurare zuwa Najeriya.

A cewar, Omo-Iduhon, akwai ‘yan Najeriya da ya wa a Italiya fiye da sauran kasashen Turai, kuma ‘yan Najeriya da su ka yi rijista bisa ga alkaluma sun kai miliyan 3 baya ga wadanda ba su da takardun shaidar izini.

“Daya daga cikin manyan matsalolin da ‘yan Najeriya mazauna Italiya ke fuskanta shi ne, karancin fasfo din Najeriya da zai taimaka wajen saukaka zirga-zirga da izinin aiki.

“Ya kamata gwamnatin Najeriya ta taimaka wajen magance wannan matsala mai cike da rudani, domin kasar Italiya ita ce hanyar shiga wasu kasashen Turai musamman ‘yan Najeriya.

“Kusan ‘yan Najeriya miliyan 1.5 a Italiya ba su da fasfo, har ma da wasu daga cikin wadanda gwamnatin Italiya ta karba ba a ba su fasfo na Najeriya ba, wanda ke da wahala su yi aiki a kasar”. Inji Omo-Iduhuon.

Ya ce kungiyar ta himmatu wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ya kara da cewa dole ne mambobin kungiyar su yi iya kokarinsu na komawa gida domin gina Najeriya.

 

A cewarsa, yawancin ‘yan Najeriya a Italiya suna da halaltaccen kasuwanci kuma ‘yan Italiya sun kasance masu karbar baki.

 

thisdaynews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp