fidelitybank

Mayakan ISWAP sun kona mutane da ransu a Borno

Date:

A na fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukan su yayin da wasu su ka jikkata, sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram su ka kai yankin karamar hukumar, Askira Uba da ke Jihar Borno.

Bayanai sun ce mayakan sun kutsa kauyen Kilangal, mahaifar mataimakin kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Injiniya Abdullahi Musa da tsakar ranar Lahadi, inda su ka cinna wa gidaje wuta.

Majiyar rahoton ta ce wani jirgin yaki na dakarun sojin sama ya kai dauki kauyen sa’o’i biyu, bayan aukuwar lamarin, sai dai tuni aikin gama ya gama.

A cewar majiyar, mayakan sun ci karensu babu babbaka a yayin da babu wata tirjiya da su ka fuskanta, inda a ke zargin cewa, mutane da dama sun tsere cikin jeji yayin da kuma wasu masu karar kwana ta cimma su.

A watan Nuwamba ne mayakan kungiyar, ISWAP masu ikirarin jihadi a yammacin Afirka suka ka yi dauki ba dadi da dakarun sojin Najeriya a karamar hukumar, Askira Uba da ke Borno.

Aminiya ta rawaito cewa, mayakan sun yi wa Askira/Uba dirar mikiya ne da misalin karfe bakwai na safiya a cikin jerin gwanon motoci da su ka kai akalla 16, inda suka yi luguden wuta a yankin Ngude.

Wasu majiyoyi sun ce mazauna sun sanar da hukumomi game da shigowar mayakan amma ba a dauki mataki ba har suka fara bude wuta a yankin.

 

latest news in lokoja, kogi state

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp