Mayakan Boko Haram sun kai hari kauyen Jibwiwi a karamar hukumar Hawul da ke jihar Borno.
Mayakan sun kona gidaje da dama tare da kona rumbunan hatsi.
Rahotanni sun ce an kona a kalla gidaje takwas da rumbunan hatsi da ya kunshi Dawa da Masara da sauran nau’ukan hatsi da dama.
’Yan Boko Haram din sun je kauyen ne a kan babura da yammacin ranar Litinin.
Kuma sun kona rumbunan ba tare da daukar komai ba.
Wani dan kungiyar sintiri a kauyen ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, bayan mayakan sun kona gidaje da rumbuna a kauyen, sai suka wuce zuwa garin Ngulde da ke karamar Hukumar Askira Uba, to amma sun murkushe su da taimakon mafarautar yankin.