A kalla ‘yan ta’addar Boko Haram 204 ne da ‘yan uwansu suka mika wuya ga sojojin Najeriya, ta hanyar Operation Hadin Kai a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
A cewar rundunar sojoji ta kasa a ranar Laraba, ta ce, ana ci gaba da bayyana ‘yan ta’addar Boko Haram da suka mika wuya. In ji PM News.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Harin da ake ci gaba da kai wa ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas ya sake yin wani gagarumin nasara a ranar 15 ga watan Yuni, 2022, yayin da mayakan Boko Haram 204 ciki har da ‘yan uwansu suka mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai a karamar hukumar Bama ta jihar Borno. Ana ci gaba da bayyana ‘yan ta’addan da suka mika wuya”.