A Iraki an baiwa ma’aikatan gwamnati a jihohi da ke tsakiya da kudancin kasar hutun kwana guda, bayan da yanayin zafi ya kai digiri 50 na maunin celtuis.
An rufe ofishoshin gwamnati a birnin Bagadaza sai dai matakin bai shafi jamain tsaro da wadanda suke ayuika na musaman ba. In ji BBC.
A garin Basra mai tashar jirgin ruwa an ayanna hutun kwanaki hudu.
Matsanancin zafi ba sabon abu ba ne a Iraƙi saboda yana daya daga cikin wurare mafiya zafi a duniya.
Sai mazauna yankin sun ce, lamarin yana kara yin muni ta hanyar daukewar wutar lantarki wanda ya sa ba a samun nauarar sanyaya iska watau AC.
Sun kuma ce, alamarin na kara ta’azzara a kowace shekara.


