matatar mai na Kamfanin Dangote wanda zai rinƙa samar da 650,000 a kowace rana (bpd) da ake ginawa a Najeriya zai fara hako mai a shekarar 2022, in ji Babban Darakta Devakumar Edwin a ranar Lahadi.
Edwin ya bayyana hakan ne yayin wani rangadi da ministan yada labarai, Lai Mohammed ya yi. Ya ce, “Kashi 75 cikin 100 na gwajin ruwa da kuma kashi 70 cikin 100 na na’urorin sadarwa na lantarki an kammala shirye-shiryen, kammala aikin matatar a cikin kwata na hudu na wannan shekara,”
Matatar man da aka gina kan kudi dala biliyan 19 a Legas, tana da karfin ajiyar lita biliyan 4.74 inji Edwin. Ya kara da cewa, kashi 75 cikin 100 na kayayyakin za a rika jigilar su ne ta ruwa a cikin Najeriya.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote ya ce, a watan Janairu yana sa ran aikin matatar mai zai fara hakowa a karshen kwata na uku kuma ya kai gaci nan da farkon shekarar 2023.
An jinkirta aikin da shekaru da yawa kuma kudin ya kai dala biliyan 19 daga kiyasin da Dangote ya yi a baya na dala biliyan 12 zuwa dala biliyan 14.