fidelitybank

Matashi ya yi garkuwa da yarinya ya kuma yanka ta a Kano

Date:

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da ya yi garkuwa da wata yarinya yar kimanin shekaru 13 da haihuwa, har sai da ya kashe ta saboda ya fahimci cewa yarinyar ta gane shi.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce”A ranar 21/06/2021 sun samu rahoto daga wani mazaunin garin Tofa da ke ƙaramar hukumar Tofa a jihar Kano, cewa an yi garkuwa da ‘yarsa mai suna Zuwaira mai shekaru 13 tare da buƙatar ya bayar da kuɗin fansa naira miliyan daya. Daga baya a ka koma Naira 400,000.00.

“Yayin da a ke tattaunawa domin neman kudin fansar, sai aka gano gawar yarinyar a wani kango inda aka yankata kuma aka binne a wajen.

”Bayan samun rahoton, an ziyarci wurin, a ka tono gawar, likitoci kuma suka tabbatar da mutuwar ta, inda muka mika gawar ga ’yan uwanta don a yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada”. Inji kiyawa

Sanarwa ta kuma ce hakan tasa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umurci rundunar ‘Operation Puff Adder’ ƙarƙashin jagorancin SP Shehu Dahiru waɗanda Allah ya basu ikon kama wanda ake zargi da aikata laifin wato Auwalu Abdulrashid, wanda ake kira da Lauje, Dan kimanin shekaru 21 a ƙauyen Ɗan Marke kauyen Dan Marke.

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp