fidelitybank

Matashi ya yi garkuwa da kansa ya karbi kudin fansa 70,000 – ‘Yan sanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin wani mutum da ya yi garkuwa da kansa domin karbar kudin fansa a wurin mahaifin sa.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis ga manema labarai.

Ya ce,”Sunan sa Hayatu Musa dan asalin garin Madobi a Kano, mahaifinsa ya kawo mana kara cewa masu garkuwa da mutane sun kama dansa tare da ya biya Naira Dubu Dari kudin fansa kafin a sake shi, bayan mun yi binciki mu ka gano kuma zancen ba haka bane”. A cewar SP Kiyawa.

Sai dai wanda a ke zargin mai suna Hayatu Musa ya tabbatar da cewa,”Ni da kai na ne na yi garkuwa da kai na babu wanda ya yi garkuwa, kuma na make murya ta, sannan na kirawo mahaifi na a waya na shaida masa halin da a ke ciki”.

A nasa jawabin mahaifin matashin ya ce,”Mun yi waya da masu garkuwa dama kudin da su ka bukata in ba su, a she da na ne da kansa ya makale murya ya kira ni domin ya karbi kudinsa”.

 Daga baya dai sai da mahaifin sa ya biya kudin fansa Naira Dubu Saba’in a wajen mahaifin na sa, kamar yadda rundunar ta tabbatar da hakan.

latest news in lokoja, kogi state

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp