fidelitybank

Matashi dan Jigawa ya rataye kansa a bishiya

Date:

Rundunan ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da wani mutum mai shekara 25 da ya kashe kansa ta hanyar rataya a wani gari da ke karamar hukumar Taura.

mai magana da yawun rundunar, ASP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce, mutumin wanda da farko aka bayar da rahoton batansa, an same shi ya rataye kansa ne a wata bishiya da ke bayan gari a kauyen Zangon Maje na karamar hukumar, inda ya yi amfani da wandonsa a matsayin igiya, a jiya Litinin, 24 ga watan Janairu, 2022.

Ya ce, a ranar Litinin ne Hakimin Kwalam, Alhaji Muttaka Uba ya kira su inda ya sheda musu cewa, wani mutum Naziru Badamasi, mai shekara 25 na kauyen Tsadawa da ke karamar hukumar Taura, wanda kuma ya ke da tabin hankali, ya bata bayan ya bar gida a ranar da misalin karfe goma sha biyu da rabi na rana.

ASP Shiisu ya ce, daga bisani ne aka gano mutumin ya rataye kansa a bayan garin kauyen Zangon Maje, wanda shi ma a yankin wannan karamar hukuma yake.

Kakakin ya ce, da samun wannan labari aka tura jami’an ‘yan-sanda suka je wurin, inda suka dauko gawar suka kai ta babban asibitin Ringim, inda likita ya tabbatar da cewa mutumin ya rasu.

Jami’in ya kara da cewa, daga baya ne suka mika wa ‘yan uwan mamacin gawar domin yi masa jana’iza kasancewar binciken farko-farko da suka yi ya nuna cewa ba wani zargi da ake na wata makarkashiya kan mutuwar.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka Æ´an Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation HaÉ—in-Kai sun ce sun kashe Æ´an...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aÆ™alla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naÉ—a shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp