fidelitybank

Mata ta kashe kanta a Kano ta hanyar caka gilashi a makogaronta

Date:

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wata mata da a ke zargin ta kashe kanta a unguwar Sheka da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

‘Yan sandan dai sun ce matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fasasshen gilashin taga na Luba, ta yanka kanta bayan gartsa wa mahaifinta cizo, sannan ta gutsire dan yatsanta da ke ciwo na Karkare.

Wani dan uwan marigayiyar mai suna, Muhammad Sanusi, ya ce“Kafin ‘yar uwar ta wa ta su ta kashe kanta ta yi fama da ciwon yatsa wato karkare, wanda har sai da ta kai ga mun rufe ta a ɗaki na tsawon kwana biyar, sakamakon yadda ta koma tamkar mai taɓin hankali, a ranar da mu ka buɗe ta ne ta fasa gilashin tagar ɗakin da a ka rufe ta sannan ta yanka kanta a makogoro”.

A shekarar 2021 an samu mutane sama da biyar da suka kashe kansu a Kano, wanda wasu daga cikinsu aka alaƙanta su da matsalar ƙwaƙwalwa.

Na baya-bayan da aka samu shi ne na wani matashi da ya kashe kan sa ta hanyar yanke al’aurar sa, a cewar BBC.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp