fidelitybank

Masu garkuwa sun saki shugaban ASUU da dan takarar gwamna

Date:

Masu garkuwa da mutane sun sako shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), reshen jami’ar jihar Filato, Hassan Zitta, da tsohon dan takarar gwamna a jihar, Nicholas Nshe.

Sakataren kungiyar, Samson Deme ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Premium ta wayar tarho.

Ya ce,”An sako mutanen biyu ne a daren ranar Talata bayan sun shafe kwanaki 11 a wurin masu garkuwa da mutane. Akalla an biya kudin fansa Naira miliyan 10 kafin a sako su.

Ya kuma ce, “Bayan an biya Naira miliyan 10 ba a sake su ba. Sai da suka kara wasu kudi domin a sake su, amma ban san nawa ba.” An samu labarin cewa masu garkuwan sun bukaci kimanin Naira miliyan 90 yayin da su ka bukaci Naira miliyan 50 ga tsohon dan takarar gwamnan da kuma Naira miliyan 40 ga shugaban ASUU domin a sako su”.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin Ubah Ogaba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato ba.

Mutanen biyu sun shafe kwanaki 11 tare da wadanda suka sace su bayan an yi garkuwa da su a jajibirin sabuwar shekara a gidan tsohon dan takarar gwamna kuma tsohon shugaban karamar hukumar Shendam, Mista Nshe.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp