Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari wani yankin Jibia, jihar Katsina tare da saka wa jama’a harajin Naira 10,000 a yankin.
Rahotanni sun ce, an kai harin a wani yankin da a ke sarrafa Gwal, inda a ka sace wasu mutane da yawa a wurin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce ta na nan ta na ci gaba da bincike.
Rahotanni na nuni da cewa, ’yan ta’addar sun sanya harajin Naira 10,000 a yankin sarrafa Gwal da ke karamar hukumar Jibia a Jihar Katsina, domin ci gaba da hako ba tare da tasgaro ba. Wurin ya na cikin al’ummar Bakin Korama a garin Magama Jibia kan iyakar yankin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, akalla kananan cibiyoyin sarrafa Gwal 70 ne ke gudanar da aiki a wurin, wanda a ka bude kimanin makwanni biyu da suka gabata.