fidelitybank

Masarauci mafi daɗewa a masarautar Kano,  Sarkin Bai Adnan ya rasu

Date:

 

Sarkin Ban Kano, Tsohon Hakimin Ɗambatta, Dakta Mukhtar Adnan ya rasu.

Marigayi Adnan, ya rasu ya na da shekara 95 a wani asibiti da asubar yau Juma’a a Kano.

Kafin rasuwarsa, marigayin shine Kwamishinan Ilimi na farko a tarihin Kano.

Dakta Adnan ya kasance ɗan majalisar Sarki tun a shekarar 1954.

Marigayin ya kuma kasance ɗaya da ga cikin masu naɗin Sarki, inda da shi a ka naɗa Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero a 1963.

Tun a 1953 marigayi Adnan ya zama Hakimin Ɗambatta har zuwa shekarar 2019, inda a ka cire daga hakimcin sakamakon sabuwar dokar masarauta da Gwamna Abdullahi Ganduje ya ƙirkiro.

Wannan jarida ta jiyo cewa da safen nan ne dai za a yi jana’izar Sarkin Bai kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a sanar da lokacin da za a yi jana’izar marigayin ba.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp