fidelitybank

Sarkin Ban Kano: Mukhar Adnan ya rasu ya na da shekaru 95

Date:

Sarkin Ban Kano kuma hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan ya rasu, sakamakon gajeriyar rashin lafiya da ya yi a ranar Juma’a.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da rasuwar mariyai Mukhtar Adnan mai shekaru 95, a safiyar ranar Juma’a, inda ta ce ya rasu kwanaki biyu bayan jinyarsa a wani asibiti mai zaman kansa, UMC Zhahir, a Kano.

Ya rasu ne da misalin karfe 4 na safiya, kwana biyu kacal bayan an sallame shi. Za a yi Jana’izarsa a yau bayan Sallar Juma’a a Dambatta.

Sarki Muhammadu Sunusi na Daya ne dai ya nada shi a matsayin Sarkin Bai a shekarar 1954 marigayi sarkin ya halarci zaben sarakunan Muhammadu Inuwa a watan Afrilu 1963, Ado Bayero a watan Oktoba 1963, Muhammadu Sanusi II a watan Yuni 2014 da kuma Aminu Bayero a watan Maris 2020.

An haifi Alhaji Mukhtar Adnan a shekarar 1926 kuma tsohon sarkin Kano Sir Muhammad Sanusi ne ya naɗa shi a matsayin sarkin Bai a shekarar 1954 domin ya gaji mahaifinsa Sabon Dambazau.

Marigayi Sarkin Bai shi ne kwamishinan ilimi na farko a jihar Kano a 1968, kuma ya halarci makarantar Elementary da ke Ɗambatta da makarantar Midil ta Kano da kuma makarantar malamai a garin Zaria.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp