fidelitybank

Manchester City ta yi wasan kura da Liverpool

Date:

Manchester City ta casa Liverpool da ci 4-1 ranar Asabar da rana a filin wasa na Etihad, duk da rashin zaƙaƙurin ɗan wasanta na gaba Erling Haaland.

Haaland  wanda ya ci wa Man City ƙwallo 42 a kakar wasa ta bana – yana fama da rashin lafiya.

Sai dai, duk da haka ƙungiyar ta nuna irin ƙarfin da take da shi bayan ta farke ƙwallon da Liverpool ta fara jefa mata a raga.

A cikin minti na 17 da take wasa, Liverpool zura wa City ƙwallo ta hannun Mo Sallah.

To amma a minti na 27, Julian Alvarez – wanda ya fara wasan a madadin Erling Haaland – ya farke wa City, bayan Jack Grealish ya bugo ƙwallon ta gefe.

A cikin daƙiƙa 53 bayan komawa hutun rabin lokaci ne kuma, Kevin De Bruyne ya zura ƙwallo ta biyu, lokacin da Mahrez ya tura masa ƙwallo.

Ana minti na 53 kuma, Ikay Gündogan ya ƙara ta uku, bayan ya tsinci wani ƙwallo da Alvarez ya buga a da’irar yadi na 18.

Kafin daga bisani Jack Grealish – wanda ya kasance gwarzon ɗan wasa a karawar – ya zura tasa ƙwallon bayan Kevin De Bruyne ya gara masa bal.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...
X whatsapp