fidelitybank

Man Fetur: Kungiyar Kwadago za ta tsunduma yajin aiki a sabuwar shekara

Date:

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta bayyana shirin fara shiga zanga-zanga a fadin kasar a ranar 27 ga watan Janairu na 2022, domin nuna adawa da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na kara farashin man fetur.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da babban sakataren kungiyar, Kwamrade Emmanuel Ugboaja, ya aikewa shugabannin kungiyoyin a jihohi 36 na tarayya.

Wasikar ta bukaci shugabannin zartaswa da su kira taron majalisar zartarwa ta Jihohi (SEC) inda za su tsara dabarun tabbatar da nasarar aikin a jihohinsu.

A wani mataki kan kudurin cewa, za ta jagoranci zanga-zangar a Jihohi 36 na Tarayyar Najeriya a ranar 27 ga watan Janairu 2022, domin nuna adawa da shirin da gwamnatin tarayya ta yi na kara farashin man fetur’.

Sanarwar ta kuma ce,“Za ku iya tunawa cewa Majalisa ta gudanar da taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) a ranar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021, inda a ka dauki wasu muhimman shawarwari. A ci gaba da wadannan hukunce-hukuncen ne mu ka rubuta, domin sanar da ku cewa ranar 27 ga watan Janairu, 2022, mu ka tsayar a matsayin ranar da Majalisar za ta gudanar da zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin tarayya na jihohi 36 na tarayya a kan kara farashin man fetur.

“An bukaci ku da ku kira taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC) inda za ku tsara dabarun tabbatar da nasarar aikin a jihar ku. An kuma ba ku kwarin gwiwa da ku tuntubi abokan zamanmu na jama’a a jiharku a kokarin ku na gudanar da wannan gangamin”.

Tun da farko, wata gamayyar kungiyoyi masu rajin kafa Ma’aikata (Mass Workers Party) da kuma ‘yan Socialist Transformation of Nigeria, wato People’s Alternative Political Movement (TPAP-M), sun yi fatali da karin farashin iskar gas da kuma shirin da ke taf na. karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki da dai sauransu.

Gamayyar kungiyoyin ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta fitar a taron jama’a da kungiyar TRAP-M da takwarorin ta su ka shirya kan karin farashin man fetur da wutar lantarki da ke gabatowa.

Ta ce za ta sake shirya wata zanga-zangar mamaya a Najeriya a bikin cika shekaru 10 na farko a watan Janairun 2022.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp