fidelitybank

Malaman jami’o’i ku koma bakin aiki ko kuji a jikin ku – Gwamnatin Gombe

Date:

Hukumar gudanarwar ta jami’ar jihar Gombe, ta bukaci malaman jami’ar da su koma bakin aiki ko kuma ta dauki matakin nan na dakatar da albashin malaman da suka bijire.

Hukumar gudanarwar ta yanke wannan shawarar ne bayan wani zama da ta yi da kungiyar malaman, kana ta tsayar da ranar tara ga wannan watan na Satumba domin fara karatu gadan-gadan.

Mahukunta a jihar Gombe sun bayyana cewa duk wata kara da karamcin da ya kamata sun yi wa malaman jami’ar jihar a tsawon lokuta daban-daban da kungiyar malaman jami’a ta kasa ta kwashe mambobinta na yajin aiki, kasancewar gwamnatin jihar ba ta hana wa malaman ko da sisin kwabo ba, duk kuwa da cewa ba da ita suke fada ba.

Don haka ne ta nemi malaman jami`ar jihar da su fahince cewa tuwon girma miyarsa nama – kuma idan duniya da gaskiya to ya kamata a yi wa mazari riga da wando.

Bisa al`ada dai malaman da ke jami’o’i na jiha sukan yi biyayya ga uwar kungiyar ta kasa a duk lokacin da aka bukace su ko da kuwa matsalar ba ta shafe su kai-tsaye ba, kuma suna hakan ne saboda su gudu tare su tsira tare.

Kawo yanzu kungiyar malaman jami’ar jihar Gomben ba su ce uffan ba kan umarnin na gwamnati.

Sama da watanni 6 kenan da malaman jami`o`in gwamnatin Najeriya suka tsunduma yajin aiki, bayan wadanda suka yi a lokuta daban-daban da kulla yarjeniyoyi da dama tsakaninsu da gwamnati.

Sai dai har yanzu bangarorin biyu ba su daidaita ba, kuma dalibai ne ke shiga tsaka mai wuya kan yajin aikin.

latest news in nigeria today 2022 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp