fidelitybank

Makamai: EU za ta kakabawa Myanmar sabon takunkumi

Date:

Kungiyar tarayyar Turai ta ce a shirye take ta kakaba wa kasar Myanmar karin takunkumi bayan wani sabon tashin hankalin da sojojin kasar su ka yi, sannan kuma ta bukaci da a kakabawa kasar takunkumin siyan makamai.

Hukumomin jin kai sun bayyana karara cewa  sama da mutane 30 da suka hada da mata da kananan yara ne sojoji suka kashe tare da kona gawarwakinsu a wani kauye da ke jihar Kayah da ke fama da rikici a kasar Myanmar a makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaitoo cewa, rundunar sojin Myanmar ta ce ta kashe wasu ‘yan ta’adda da makamai da ba a tantance adadinsu ba daga dakarun ‘yan adawa a wani kauye, bayan da su ka ki tsaya a shingin binciken sojojin, domin bincikar su..

A cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar EU, Josep Borrell ya fitar a ranar Alhamis dinnan, ya ce “Saboda karuwar tashe-tashen hankula a Myanmar, a na bukatar kara daukar matakan kariya daga kasashen duniya, gami da sanya takunkumin makamai.”

Ya kara da cewa “EU kuma a shirye ta ke ta kara sanyawa gwamnatin soja takunkumi.”

Tun bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a watan Fabrairu, kungiyar EU ta kakaba wa sojojin Myanmar da shugabanninta da kuma hukumominta takunkumin karya tattalin arziki. Sannan EU ta  dakatar da taimakawa kasar ta fannin kudi.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp