fidelitybank

Kafa Gwamnati: Sabuwar majalisar dokokin Iraqi za ta gana a sabuwar shekara

Date:

Shugaban kasar Iraqi ya sanar da cewa sabuwar majalisar dokokin kasar za ta yi zama a ranar 9 ga watan Janairu, kan yadda ‘yan majalisar za su kafa sabuwar gwamnatin kasar Iraq

A wata doka da shugaba kasar, Barham Salih ya fitar a ranar Alhamis, ta shirya yadda ‘yan majalisar za su kafa sabuwar gwamnati.

A cikin wata sanarwa da hukumomin kasar su ka fitar a ranar Alhamis dinnan, ‘yan majalisar za su zabi kakakin majalisa da mataimaka biyu a zamansu na farko. Daga baya kuma za su zabi sabon shugaban da zai dora wa jagoran babbar kungiyar kafa gwamnati a matsayin firaminista.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, babban wanda ya lashe zaben na ranar 10 ga watan Oktoba shi ne malamin Shi’a, Moqtada al-Sadr, mai ra’ayin jama’a wanda ya sanya kansa a matsayin dan adawar Iran da Amurka.

Kungiyar Sadr, wacce tuni ta kasance mafi girma a majalisar dokokin kasar mai kujeru 329, za ta fadada zuwa kujeru 73 daga 54. Manyan abokan hamayyarta na tsawon shekaru, kungiyar Fatah da ke da alaka da mayakan sa kai na Tehran, a halin da a ke ciki, wakilanta na majalisar sun ruguje zuwa kujeru 17 kacal daga 48.

Shugabannin siyasar kungiyar ta Fatah sun gudanar da wani taro da malamin addini Sadr a gidansa da ke birnin Najaf a kudancin kasar su ka tattauna batun kafa gwamnati, sai dai ba a fitar da wani kwakkwaran sakamako bayan taron.

Sai dai kuma babu wani kawance da ya samu rinjaye, kawancen ‘yan Shi’a da Sunni da Kurdawa sun wanda suka  yi ta raha a sabuwar gwamnati.

thisday nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp