Majalisar dattijai a ranar Talata, ta dakatar da zamanta kan mutuwar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Egor/Ikpoba-Okha a Edo, Jude Ise-Idehen.
Ise-Idehen, har zuwa rasuwarsa, dan majalisar wakilai ne a karkashin jamâiyyar PDP.
Majalisar dattijai da ta dawo daga hutun makonni biyu, ta dage zamanta zuwa ranar 20 ga watan Yuli, domin karrama marigayin wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Yuli yana da shekaru 52 a duniya.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sen. Ajayi Boroffice (APC-Ondo) ne ya gabatar da kudirin dage zaman, sannan shugaban marasa rinjaye, Sen. Philip Aduda (PDP-FCT) ya goyi bayansa.
Majalisar dattijai, ta kuma yi shiru na minti daya don makokin marigayin kafin ta dakatar da zaman majalisar.
Majalisar ta samu jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege (APC â Delta Central).