fidelitybank

Mai Twitter ya nada ‘yan Najeriya 3 da za su jagoranci raba kudin Bitcoin

Date:

Mamallakin shafin sada zumunta na Twitter, Jack Dorsey, ya nada wasu ‘yan Najeriya Uku, da za su jagoranci shugabancin asusun amincewar Bitcoin.

Jack Dorsey, daya daga cikin wadanda suka kirkiri shafin Twitter ya nada ‘yan Najeriya uku da daya dan Afirka ta Kudu da su zama hukumar kula da asusun sa na Bitcoin Trust (BTrust) da za a raba domin ci gaban Afirka da Indiya.

A farkon watan Fabrairu, Dorsey ya ba da sanarwar BTrust tare da haɗin gwiwar mawakin gambara na rap dan Amurka, Jay Z.

BTrust asusu ne da ke da babban asusun BTC 500 wanda darajarsa ta kai N10,014,265,775.40 ($24,426,230), idan aka kwatanta shi da farashin kasuwar ranar Litinin dala $48,815.35, kuma ‘yan Afirka hudu ne za su sarrafa su, ba tare da kulawa daga Dorsey ko Jay Z ba.

A ranar Laraba, 15 ga watan Disamba, Dorsey ta wata sanarwa ya bayyana sunayen hukumar ta BTrust, wadanda uku daga cikinsu ‘yan Najeriya ne; Abubakar Nur Khalil da Obi Nwosu da Ojoma Ochai, da kuma Afirka ta Kudu, Carla Kirk-Cohen.

Idan za a iya tunawa a karshen watan Nuwamba, Dorsey ya yi murabus a matsayin shugaban Kamfanin Twitter.

Mista Dorsey, wanda ya kafa Twitter a 2006 tare da Biz Stone, Evan Williams, da Noah Glass ya na aiki a matsayin shugaba na Twitter da kuma kamfanin biyan kuɗi Square.

A cikin wata sanarwa da a ka fitar, ya rubuta, “Lokaci ya yi da zan tafi”, lura da cewa kamfanin “a shirye ya ke ya ci gaba.”

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp