Wani tosho ɗan shekara 86 ya karya tarihi a gasar ɗaga ƙarafa ta duniya.
Mutumin mai suna Brian Winslow ya ɗaga karfe mai nauyin kilogram 75 a gasar ɗaga ƙarafa ta Birtaniya wanda aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris 2023.
Brian Winslow wanda ya fito ne daga yankin Derbyshire ya kafa tarihi ne bayan ɗaga karfe mai nauyin kilogram 77 a karon farko.
Mr Winslow a yanzu shi ke riƙe da tarihi gasar a Birtaniya da kuma duniya a ajin ƙarafa masu nauyi na kilogram 60 a ɓangaren maza masu shekara 85 zuwa 89.
Mr Winslow, wanda ya fara ɗaga ƙarafa tun yana matashi lokacin da yake aiki a wani gidan sayar da abinci, ya ce ya yi farin-ciki da tarihi da ya kafa.
“Abu ne mai kyau wajen kafa tarihi. Ɗaga ƙarafa yana cikin wani ɓangare na rayuwata haɗe da ‘ya’yana da kuma jikoki. Zan kuma ci gaba da ɗaga ƙarfe har sai lokacin na koma bana iyawa.” in ji Winslow