Wani mahaifi mai shekaru 49, Amoda Bola, ya yi wa diyarsa mai shekaru 14 ciki a Ode, karamar hukumar Remo ta Arewa a jihar Ogun.
‘Yan sanda sun cafke mahaifin a Ogun. Wanda ake zargin, mazaunin unguwar Idi Oro, Ode Remo, an kama shi ne biyo bayan wani korafi da aka samu daga wanda abin ya shafa.
‘Yar ta shaida wa ‘yan sanda cewa “mahaifinta, wanda ta shafe shekaru da yawa tare da ita, ya kasance yana sanin ta ta jiki,” in ji kakakin ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi a ranar Lahadi.
A cewar Oyeyemi, yarinyar ta shaida wa ‘yan sanda cewa “mahaifin nata ya kuma rika gayyatar wasu maza zuwa gidan domin su yi lalata da ita daga nan ne mazan za su biya shi kudi.” in ji Daily Post.


