Matsalar samar da wutar lantarki a Najeriya na iya kara ta’azzara daga gobe Laraba, yayin da kungiyar kwadago ta umarci ma’aikata a bangaren wutar lantarki da su yi watsi da kayan aiki tare da fara yajin aiki na har abada kan matsalolin da ake fuskanta na ma’aikata da kamfanin sadarwa na Najeriya (TCN).
A ranar Talata ne kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) ta yi taro a hedikwatar hukumar ta TCN da ke Abuja. In ji Daily Post.
Ma’aikatan da suka koka da yadda gwamnatin tarayya ta gaza biyan tsoffin ma’aikatan kamfanin wutar lantarki na Najeriya (PHCN) hakkokinsu a watan Disambar 2019.
Sun ce wannan wani share fage ne na yajin aikin da ake sa ran za a fara ranar 17 ga watan Agusta.