fidelitybank

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Date:

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa wani matashi Yusuf ya rasa ransa a kamfanin Mamuda Group da ke Challawa, Jihar Kano, bayan da aka ce wani supervisor ya daɓa masa wuka.

Wasu rahotonnin dai daga Social Media sun ce an sallami matashin a aiki shi ne ya je karbar kudin sallama a nan supervisor din ya caka masa wuka.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dangin mamacin ke kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike, tare da neman a tabbatar da adalci.

To amma a hirar da mahaifiyar marigayin ta yi da tashar Freedom Radio da ke Kano ta ce wanda ya caka masa wukar dama can suna da sabani tsawon lokaci.

Me kamfanin Mamuda Group ke cewa a kai?

Jamiʼin yada labaran kamfanin Bashir Alhasan Indabawa ya karyata wannan zargin cewa a kamfanin aka kashe matashi.

Ya ce, hatsaniyar ta faru ne tsakanin wasu ma’aikata biyu a wajen harabar kamfanin, kuma wanda ya caka wukar ba supervisor ba ne, dukkansu kananan maʼaikata ne a kamfanin.

Ya ƙara da cewa, suna da shaida cewa maʼaikatan su 2 sun bada uzri don fita daga kamfanin a wannan lokacin, kuma suna da bidiyo da kamfanin ya nada na duk abin da ya faru a harabarsa.

Ya ce, kuma duk da hakan ma’aikatan kamfanin ne suka kai wanda aka jikkata asibiti tare da hadin gwiwar ’yan sanda, kafin daga bisani ya rasu.

Yanzu haka dai ana ci gaba da jiran karin bayani daga rundunar ’yan sanda da sauran hukumomi, yayin da al’umma ke ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan lamarin.

Go back

Your message has been sent

Warning
Warning
Warning
Warning

Warning.

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp