Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa, lokaci na neman ƙure musu a game da batun gabas ta tsakiya.
“Rikicin da ake yi a gabas ta tsakiya ya fara zama kamar wata gobara,” kamar yadda Guterres ya bayyana wa wakilan kwamitin.
Ya ce tun makon jiya, “abubuwa suke ta ƙara lalacewa.”
Ya ce Isra’ila ba ta sassauta hare-harenta a Lebanon, inda ya ce sun fara tunanin samar da yarjejeniyar tsagaita na ɗan lokaci, amma sai Isra’ilar “ta ƙara ƙaimi” wajen kai hare-haren.
Ya ce shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da zaman lafiya na nan daram, sannan “tutar Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da kaɗawa a Isra’ila.”
Ya ce, “ina sake Allah-wadai da hare-haren makamai masu linzami da Iran ta ƙaddamar a Isra’ila.”
Tun farko, Isra’ila ta sanar da hana shi shiga ƙasarta, saboda a cewarta ya ƙi yin Allah-wadai da hare-haren da Iran ta kai mata.
Ya ce. “lokaci na neman ya ƙure mana,” in ji shi, sannan ya yi kira da a tsagaita wuta.


