Shahararren mai sharhi kan al’umma, Reno Omokri, ya yi ikirarin cewa tawagar lauyoyin Peter Obi na jam’iyyar Labour a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa abin kunya ne abun da suke yi.
Omokri, mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter ranar Asabar.
Omokri, babban mai goyon bayan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya ce ya ji takaicin irin shedu da hujjojin da tawagar lauyoyin Obi ta gabatar a gaban kotun.
Ya yi zargin cewa lauyoyin Obi suna yin kura-kurai ta hanyar karkatar da jadawalin takardunsu sannan kuma suna neman ƙarin lokaci.
Ya lura cewa yadda tawagar Obi ke tafiya game da koken ba zai haifar da sakamako ba.
“Tawagar lauyoyin Peter Obi da shaidun su a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa abin kunya ne kawai.


