Daruruwan direbobin manyan motoci sun rufe babbar hanyar Auchi zuwa Benin, domin nuna damuwarsu a kan lalacewar hanyar.
Direbobin sun rike kwalaye da ke dauke da rubuce-rubuce na korafi, inda datse hanyar a daidai fitacciyar mahadar nan ta Jattu, da ke yankin Karamar Hukumar Etsako West ta Jihar Edo, abin da ya hana motoci da matafiya wucewa.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa zanga-zangar ta haddasa cunkoson motoci a tagwayen hanyar, inda jerin ababan hawa ya zarta tsawon kilomita biyu.
Da yake magana a madadin direbobin, Mista Donald Etamobe, ya ce za su ci gaba da zanga-zangar har sai gwamnatin tarayya ta ji kukansu.
Ya ce ba su da zabi ne da ya wuce su dauki wannan mataki saboda titin ya lalace matuka har ta kai ba a iya binsa.


