fidelitybank

Lakurawa cikakkun ‘yan Ta’adda ne – Gwamnati

Date:

Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyuka tare da ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ta ƴanta’adda.

Lakurawa ƙungiya ce ta ƴanbindiga da sunanta ya yi amo a bara, duk da cewa mazauna yankunan Sokoto da Zamfara da Kebbi da suke maƙwabtaka da Nijar sun ce sun daɗe suna shigowa jefi-jefi.

A takardar ƙara da gwamnatin ta shigar a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, ta zargi ƴan ƙungiyar da aikata ayyukan ta’addanci da sata da garkuwa da mutane da kai hare-hare kan jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati.

Ta kuma zargi ƴan ƙungiyar da gurɓata tunanin mutane, ta hanyar ba su shawarar yi gwamnati bore.

Ministan shari’ar Najeriya, Leteef Fagbeni ya ce ƴan ƙungiyar na barazana ga tsaron Najeriya, wanda hakan ya sa suka buƙaci kotu ta haramta ayyukanta, tare da ayyana ta a matsayin ta ƴanta’adda.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a James Omotosho, ya haramta ayyukan ƙungiyar sannan ya ayyana ta a matsayin ta ƴanta’adda.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp