Donald Trump ya rattaba hannu kan wata dokar zartarwa ta sakin dukkan wasu bayanai da suka shafi kisan gillar da aka yi wa Shugaba John F Kennedy da ɗanuwansa Bobby Kennedy da kuma jagoran ƴantar da baƙaƙen fata a ƙasar Martin Luther King, nan take.
Har yanzu dai ana tababa kan harbin da aka yi wa Shugaba Kennedy a Dallas a 1963, inda wasu ke zargin da sa hannun Cuba.
A halin da ake ciki dangin Martin Luther King sun yi zargin cewa kisan nasa wata maƙarƙashiya ce ta gwamnatin Amurka.
Shugaba Trump ya ce yanzu komai zai bayyana ga jama’a.