Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya caccaki ‘yan siyasar Najeriya kan ci gaba da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.
Musa ya caccaki ‘yan siyasar a shafin sa na Instagram ranar Talata, ya kuma tambayi yadda suka ji a lokacin da suka fita kasar waje, domin ziyartar makarantun ‘ya’yansu, yayin da daliban Najeriya ke makale a gida.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, yajin aikin ASUU ya shiga wata na biyar, inda ba a ga ci gaba da yajin aikin ba saboda har yanzu malaman ba su sauya wasu bukatu ga gwamnatin tarayya ba.
A ranar litinin da ta gabata ne shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya kai ziyara garin Daura na jihar Katsina domin gudanar da bukukuwan Sallah, ya koka da yajin aikin da ya yi yana mai cewa ya isa a ajiye dalibai a gida.