Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta karyata rahotannin da ke cewa tana daukar ma’aikatar.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Asabar
Ta ce wasu ‘yan damfara ne suka tsara wannan sanarwar da ke neman yaudara da kuma amfani da jama’ar da ba su ji ba su gani ba, wajen raba dukiyar da suka yi ta kud’i don neman guraben aiki.
Hukumar ta ci gaba da cewa, a halin yanzu ba ta yin wani aikin daukar ma’aikata ko kadan kuma jama’a su yi watsi da wallafe-wallafen.
Ya ba da tabbacin cewa, ana ci gaba da kokarin zakulo wadanda ke da irin wadannan labaran na yaudara da nufin gurfanar da su a gaban kuliya.