Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar sabuwar jam’iyya ta NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kai ziyarar ta’aziya ga al’ummar Ondo kan harin cocin St Francis Catholic da ke Owo.
Harin ya yi sanadin rayukan masu ibada sama da 40, lokacin da ‘yan bindiga suka farwa coci makwanni biyu da suka gabata.
Sanata Kwankwaso a lokacin ziyarar, ya yi kira ga gwamnatin Tarayya ta sake nuna jajircewa wajen tabbatar da tsaron Najeriya da al’ummarta, yana mai cewa tsaron kasa shi ne abu na farko a ko da yaushe.
Masarautar Owo ta jinjinawa wannan ziyara ta Kwankwaso. In ji BBC.