fidelitybank

Kwankwaso ka yi murabus ko jam’iyya ta kore ka – Ƙungiyar Shugabannin NNPP

Date:

Kungiyar shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), ta bukaci dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya yi murabus cikin gaggawa ko kuma a dakatar da shi har abada, saboda zarginsa da hannu a cikin ayyukan cin hanci da rashawa.

Shuwagabannin jam’iyyar sun nemi a yi masa cikakken bayani game da abin da suka bayyana a matsayin “alaka marar kyau tsakanin Kwankwaso da jam’iyyar APC a lokacin da kuma bayan babban zabe.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Sunday Oginni ya fitar, ya zargi Kwankwaso da laifin kitsa rikicin NNPP a fadin kasar nan, a wani yunkuri na kwace jam’iyyar daga ainihin mai su da kuma wadanda suka kafa jam’iyyar.

Sanarwar ta ce, shugabannin jam’iyyar NNPP sun gano cewa, Kwankwaso tare da hadin gwiwar kungiyarsa sun yi zargin gyara kundin tsarin mulkin jam’iyyar don taimakawa a yunkurinsu na yin garkuwa da tsarin jam’iyyar.

“Hakazalika, rashin bin ka’idar tsarin mulki na baya-bayan nan da aka ce an rusa shugabannin jihohi bakwai na Ekiti, Enugu, Neja, Kaduna Katsina, Ribas da Zamfara tun daga matakin jiha da kananan hukumomi zuwa unguwanni a lokaci guda abu ne da ba za a amince da shi ba.

Don haka muna ba Shugaban riko na kasa ba bisa ka’ida ba kuma Sakatare Oladipupo Olayoku da ake zargi da cin hanci da rashawa mara misaltuwa da wuce gona da iri da ya yi murabus da kansa ko kuma ya fuskanci abin kunya na dakatarwa.

“Kungiyar shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party suna amfani da wannan dandalin domin yin kira ga wanda ya assasa wannan babbar jam’iyya Dr. Boniface Aniebonam ya tashi tsaye wajen ganin ya janye yarjejeniyar fahimtar da Kwankwaso ya yi ya dawo da jam’iyyar mu.

Muna amfani da wannan dama don yin kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri da addu’a don bullowar sabuwar Najeriyar mu baki daya.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp