fidelitybank

Kungiyoyin kwallon kafa: Gwamnatin Kano ta raba cekin kudi Naira miliyan 96

Date:

A wani yunkuri na bunkasa harkokin wasanni a jihar Kano, Gwamnan jihar,Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya raba cekin kudi na Naira miliyan 96 ga kungiyoyin kwallon kafa 47 na jihar da ke shiga gasar kwallon kafa ta kasa.

A cewarsa, kudaden za su taimaka wa kungiyoyin masu son shiga gasar ta kasa ta kakar 2021/2022.

Gwamnan wanda mataimakinsa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta a yayin bikin da aka gudanar a ranar Talata a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano.

Ya kuma bayyana cewa dukkanin kungiyoyi 10 da za su fafata a rukunin na 1, kowacce kungiya za ta samu Naira miliyan 3, kungiyoyi 29 daga rukuni na biyu. kowanne zai samu Naira miliyan 2 yayin da kungiyoyi 8 daga ajin rukuni na 3 kowanne zai samu Naira miliyan 1.

Sanarwar mai kunshe da sa hannun Hassan Musa Fagge, wanda shine sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Wannan alkawari ne da gwamnatin jihar Kano ta yi kuma ta cikawa kungiyoyin, kamar yadda sanarwar ta tabbatar da hakan.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp