fidelitybank

Kudin da Jonathan ya bari ba za su iya rike Najeriya na tsawon makwanni 3 – Amaechi

Date:

Ministan harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce kudaden da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bari, kadan ne da ba za su iya dawwama a Najeriya ba har tsawon makonni Uku kacal.

Amaechi ya bayyana hakan ne a lokacin wani shiri mai suna ‘Hard Copy’, na gidan Talabijin din Channels

Maupe Ogun-Yusuf, shi ne wanda ya kasance a shirin kuma ya tambayi ministan ko an tattauna batun tsaro a taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako, sai ya amsa da cewa ba a tabo batun a can ba.

Da a ka kara tambayar ko shugaban ya fahimci matsalar, ministan cikin raha ya ce, “ko dan jaridan bai gane ba”.

Daga nan sai ya ci gaba da mayar da martani kan wannan tambayar, inda ya danganta talauci a matsayin babban dalilin da ke yin fashi da kuma wasu kalubalen da ke tunkarar Najeriya.

“Lokacin da ku ke magana game da ‘yan fashi da duk waɗannan mutanen da su ke kashewa. Tambaya ce a kan talauci. Kuma wannan talauci bai fara a wannan mulkin ba. Kar ku manta an sayar da mai a kan dala 110, dala 114 da 115 kowace ganga. Lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, man fetur ya fadi zuwa dala 28, kuma tun daga lokacin bai haura dala 80 kan kowacce ganga ba.”

“A matsayina na tsohon shugaban kungiyar gwamnonin (Amaechi ya taba zama gwamnan Rivers sau biyu), jami’an tsaro sun shaida min a taron da tsohon shugaban kasa ya jagoranta ciki har da tsohon ministan kudi cewa a kowane lokaci gwamnati dole ne a bar kudi a baya idan Najeriya ta fada yakin da zai dauki tsawon watanni shida.

“A lokacin da mu ka zo, ba su bar kudin da za su iya kai mu tsawon makonni uku ba. Kuma ina magana a wancan lokacin a matsayina na shugaban kungiyar gwamnonin.” A cewar Rotimi.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp