fidelitybank

Imo: An yi garkuwa da sirikin Rochas, Uche Nwosu

Date:

An shiga fargaba a jihar Imo, bayan da wasu ‘yan bindiga su ka yi awon gaba da wani sirikin tsohon gwamnan jihar, Uche Nwosu, a watai cocin mahaifarsa, Eziama Obieri a karamar hukumar Nkwerre ta jihar.

Nwosu da iyalansa sun kasance a majami’aar St Peter’s Anglican, domin nuna godiya a lokacin da ‘yan bindigar da ke aiki a cikin wata mota kirar sulke da motocin kirar Hilux, su ka far wa yankin.

PUNCH ta rawaito cewa, sun yi harbi ba kakkautawa kafin su tafi shi inda su ka nufa, yayin da jami’an tsaronsa su ka zuba ido ba tare da yin tir da ‘yan bindigar ba.

Yayin da wasu makusantan Nwosu suka yi zargin cewa an yi garkuwa da shi, wasu kuma na zargin gwamnan jihar, Hope Uzodinma ne ya shirya kama shi.

Sai dai a martanin da kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Declan Emelumba ya mayar, ya ce, babu hannun gwamnan a cikin abin da ya faru.

Yayin da Emelumba ya kasa tabbatar da ko an kama shi ne ko kuma an yi garkuwa da mutane ne, ya ce, abin dariya ne a yi zargin cewa gwamnan na da hannu a bacewar Nwosu.

Da a ka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya ce, bai san da faruwar lamarin ba.

Karin bayani dai zai biyo baya a nan gaba…..

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp