fidelitybank

Ku yi harbi kan mai uwa dawabi ga masu zanga-zanga – Shugaban  Kazakhstan

Date:

Jami’an tsaro sun sake kwato titunan babban birnin Kazakhstan a yau Juma’a, bayan kwashe tsawon kwanaki a na tashe-tashen hankula.

Tuni dai shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayevk da ke samun goyon bayan Rasha ya umarci dakarunsa da su yi harbin kan mai uwa da wabi, domin murkushe zanga-zangar da a ke yi a fadin kasar.

Kwana guda bayan da Rusha ta aike da jami’an tsaro, domin su taimaka wajen murkushe ‘yan tawayen, wanda ‘yan sandan su ka ta yi sintiri a kan titunan birnin na Almaty da su ka karbe ikon sa, duk da kawo wannan lokaci a na iya jin karar harbe-harbe.

Mutane da dama ne suka mutu tare da kona gine-ginen jama’a a fadin Kazakhstan wanda mummunan tashin hankali da tsohuwar jamhuriyar Soviet ta fuskanta cikin shekaru 30 da samun ‘yancin kai.

Rahsa ta ce sama da jiragen sama 70 ne ke jigilar sojojin Rasha zuwa cikin Kazakhstan, kuma a halin yanzu, wanda a ka sake kwace filin sauka da tashin jirgi a ranar Alhamis daga wajen masu zanga-zangar.

Rikicin dai ya janyo tsoma bakin soji da Rasha ta yi a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin kasashen Gabas da Yamma a daidai lokacin da Rasha da Amurka ke shirin tattaunawa a mako mai zuwa kan rikicin Ukraine.

Shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya zargi ‘yan ta’adda da a ka horar da su daga kasashen waje da hannu wajen tashe tashen hankula, ba tare da bayar da shaida ba.

 

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp