Wani alkali a Florida da ke Amurka ya sa an bude wasu daga cikin takardun da suka ba jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurkar FBI damar binciken gidan tsohon shugaban kasar Donald Trump, da ke Mar-a-Largo.
Mai shari’ar ya bayar da umarnin ne bayan da wasu kafafen yada labarai suka kafe cewa abu ne da ya shafi bukatar al’umma sanin bayanan da suka sa binciken.
Kawo yanzu dai abin da aka sani da ke kunshe a wadannan takardu karin bayanai ne game da takardar izinin gudanar da binciken, wadanda suka kara fayyace ainahin laifukan da ma’aikatar sharia’a ta Amurkar ke binciken tsohon shugaban Donald Trump.
Laifukan da suka hada da rike wasu bayanai na tsaron kasa da yin tarnaki ko hana gudanar da bincike na tarayya, ta hanyar fitar da wasu bayanai na gwamnati ba ta hanyar da doka ta tanada ba.
Duka wadannan sun bayyana ne bayan da wasu tarin kafafen yada labarai suka bukaci kotun ta bayar da umarnin bude takardar izinin gudanar da binciken, takardar wadda ta fayyace shedar da gwamnati take da ita kafin ta samu izinin yin binciken.
Lauyan Mista Trump ya yi maraba da hukuncin alkalin Bruce Reinhardt, amma kuma ya ce tsohon shugaban ya yi amanna akwai bukatar a bari jama’a su ga ainahin takardar izinin binciken gaba dayanta ba wata da aka sakaya wasu bayanai ba.
Yanzu mai shari’a Bruce Reinhardt ya bai wa jami’ai wa’adin mako daya, wato har zuwa ranar Alhamis na su bayar da shawara kan wadanne abubuwa ne za a iya fitarwa ga jama’a da kuma wadanda bai kamata a bayyana ba a cikin takardun. In ji BBC.


