Yau ake sa ran tsohon shugaban Amurka Donald Trump zai yi bulaguro zuwa New York daga Florida, gabannin shari’ar da ke jiransa a Manhattan gobe Talata.
Inda za a mai da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa a bayyane.
Rahotonni sun ce, Mista Trump ya yi duk abubuwan da ya saba yi a ƙarshen mako, irin su buga wasan ƙwallon sanda(Golf).
To amma duk da haka ya tuntuɓi masu ba shi shawara kan yadda zai ɓullo wa abin da ya kira maƙarƙashiyar siyasa.
Ana tuhumar tsohon shugaban Amurkan da laifin biyan wata mai shirin fina-finan baɗala dubban daloli gabannin zaɓen 2016, a matsayin toshiyar baki.
Saboda ka da ta yi magana a kan zargin da ake yi masa na yin mu’amala da ita, kafin zaɓen Amurka na 2016.
To sai dai a lokutan da dama Mista Trump ya sha musanta zargin. A cewar BBC.