Wata babbar kotun jihar Osun da ke zamanta a Ikire, ta yanke wa Philip Segun mai shekaru 42 da kuma Owolabi Adeeko mai shekaru 23 hukuncin kisa, bisa laifin kashe wani Favour Daley Oladele.
An kuma yanke musu hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samun su da laifin hada baki.
Mutum na uku da aka yankewa hukuncin, ita ce mahaifiyar Owolabi, Bola Adeeko wacce aka yankewa hukuncin daurin shekaru biyu bisa laifin cin naman mutane.
Oladele kafin ya gamu da ajalinta a hannun mutanen biyu ta kasance dalibar karshe a jami’ar jihar Legas, LASU.