fidelitybank

Kotu a Kano ta daure matashi a gidan gyaran hali a kan ya saci Talo-Talo

Date:

Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi dan shekara 23, Nura Usman, hukuncin daurin watanni biyu a gidan ajiya da gyaran hali, bisa samunsa da laifin satar Talo-Talo.

Usman, wanda mazaunin unguwar Rimin Kebe Quarters ne a Kano, an yanke masa hukuncin ne bayan ya amsa laifin sata.

Alkalin kotun, Mansur Ibrahim, ya kuma ba shi zabin biyan tarar Naira 20,000 tare da umarce shi da ya biya Naira 16,000 a matsayin diyya ga mai Talo-Talon.

Tun da farko, dai Lauyan masu shigar da kara, Abdullahi Muhammad ya shaida wa kotun cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Janairu, a Rimin Kebe Quarters da ke Kano.

Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa kai cikin gidan wanda ya kai karar inda ya saci Talo-Talo daya. Sai dai wanda a ka yanke wa hukuncin ya sayar da Talo-Talon ne a kan kudi Naira 7,000.

Mai shari’a Muhammad ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 133 na dokar shari’ar jihar Kano.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp